26 Disamba 2025 - 10:53
Source: ABNA24
Amurka Ta Dakatar Da Jirgin Ɗaukar Mai Na Venezuela 

A ƙarshe Amurka ta kwace jirgen mai uku ciki har da jirgin mai na "Bella 1" bayan sanya masa takunkumi.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Rundunar tsaron gabar tekun Amurka ta kwace jirgin mai mai suna "Bella 1" a cikin ruwan Tekun Atlantika. Jirgin ɗaukar man ba ya ɗauke da wani mai lokacin da aka dakatar da shi kuma yana cikin jerin jiragen da takunkuman Amurka ya shafa. Yunkurin rundunar tsaron gabar tekun na dakatar da jirgin ya fara ne a ranar Asabar da ta gabata, amma jirgin ya canza hanya ya nufi Tekun Atlantika.

Wannan matakin ya zo ne a matsayin wani ɓangare na matsin lambar da Washington ke yi wa fitar da man fetur na Venezuela. An riga an kwace wasu jiragen ruwa biyu, "Skiper" da "Centuries". Gwamnatocin Venezuela, Iran, Rasha da China sun yi Allah wadai da kwace jirgin, inda Caracas ta kira hakan da "fashin teku".

Your Comment

You are replying to: .
captcha